“Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba?
suna bincike ko wane ne, ko kuma wane lokaci ne, Ruhun Almasihu da yake a zuciyarsu yake ishara, sa'ad da ya yi faɗi a kan wuyar da Almasihu zai sha, da kuma ɗaukakar da take biye.
kada ku yi saurin jijiguwa a zukatanku, ko kuwa hankalinku yă tashi, saboda faɗar wani ruhu, ko wani jawabi, ko wata wasiƙa a kan cewa daga gare mu suke, cewa ranar Ubangiji ta zo.
“Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko.
Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku,