23 Alherin Ubangiji Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.
23 Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Amin.
Allah mai ba da salama kuwa, zai sa ku tattake Shaiɗan da hanzari. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.
Alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su tabbata a gare ku duka.
Gayus, mai masaukina, mai kuma saukar da dukan 'yan ikilisiya, yana gaishe ku. Arastas, ma'ajin gari, da kuma ɗan'uwanmu Kawartas, suna gaishe ku.
Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.