Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.
domin kun ji tausayin ɗaurarru, kun kuma yarda da daɗin rai da wason da aka yi muku, tun da yake kun sakankance kuna da mallaka mafi kyau, mai tabbata kuwa.
An biya ni sarai, har fi. Bukatata ta biya, da na karɓi kyautar da kuka aiko mini ta hannun Abafaroditas, baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.
Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’
Sun kuwa ji daɗin yin haka, domin hakika kamar bashi ne a kansu. Domin tun da yake al'ummai sun yi tarayya da su a kan ni'imarsu ta ruhu, ashe kuwa, ya kamata su ma su taimake su da ni'imarsu ta duniya.
Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.