18 Haka ku ma, ya kamata ku yi farin ciki, ku kuma taya ni farin ciki.
18 Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.
A kullum ku yi farin ciki da Ubangiji, har wa yau ina dai ƙara gaya muku, ku yi farin ciki.
A ƙarshe kuma 'yan'uwa, ku yi farin ciki da Ubangiji. Sāke rubuto muku waɗannan abubuwa bai gundure ni ba, ga shi kuwa, domin lafiyarku ne.
Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.
Ko da za a tsiyaye jinina a kan hadaya da hidima na bangaskiyarku, sai in yi farin ciki, in kuma taya ku farin ciki, ku duka.
Ina sa zuciya ga Ubangiji Yesu in aika muku da Timoti da wuri, don ni ma in ƙarfafa da samun labarinku.