Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Filibbiyawa 2:11 - Littafi Mai Tsarki

11 kowane harshe kuma yă shaida Yesu Almasihu Ubangiji ne, domin ɗaukaka Allah Uba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Filibbiyawa 2:11
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kowa ya bayyana yarda, cewa Yesu Ɗan Allah ne, sai Allah yă dawwama a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.


Domin a rubuce yake, “Na rantse da zatina, in ji Ubangiji, kowace gwiwa sai ta rusuna mini, Kowane harshe kuwa sai ya yabi Allah.”


Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake.


Ta haka za ku san Ruhun Allah, wato, duk ruhun da ya bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana ne da jiki, shi ne na Allah.


Saboda haka ne musamman Almasihu ya mutu, ya sāke rayuwa, wato, domin ya zama shi ne Ubangijin matattu da na rayayyu duka.


Don haka nake sanar da ku, cewa ba mai magana ta wurin ikon Ruhun Allah sa'an nan ya ce, “Yesu la'ananne ne!” Haka kuma ba mai iya cewa, “Yesu Ubangiji ne,” sai ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.


Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan.


To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.


duk da haka dai, a gare mu kam, Allah ɗaya ne, wato Uba, wanda dukkan abubuwa suke daga gare shi, wanda mu kuma zamansa muke yi, Ubangiji kuma ɗaya ta gare shi muka kasance.


Duk wanda ya ci nasara, za a sa masa fararen tufafi, ba kuwa zan soke sunansa daga Littafin Rai ba, zan ce shi nawa ne a gaban Ubana, da kuma a gaban mala'ikunsa.


“Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama.


Allah ya aiko wa Isra'ilawa maganarsa, ana yi musu bisharar salama ta wurin Yesu Almasihu, shi ne kuwa Ubangijin kowa.


“Don haka sai duk jama'ar Isra'ila su sakankance, cewa shi Yesun na da kuka gicciye, Allah ya mai da shi Ubangiji, da kuma Almasihu.”


Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a.


domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.


Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina, “Zauna nan a damana, Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.”


Gama masu ruɗi da yawa sun fito duniya, waɗanda ba sa bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana da jiki, irin wannan shi ne mai ruɗi, magabcin Almasihu.


Mutumin farko daga ƙasa yake, na turɓaya ne. Na biyun kuwa daga Sama yake.


al'ummai kuma su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa. Yadda yake a rubuce, “Domin haka zan yabe ka a cikin al'ummai, In kuma yi waƙar yabon sunanka.”


Toma ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangijina Allahna kuma!”


Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka,


Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama'a.


Domin yau an haifa muku Mai Ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji.


A zamaninsa za a ceci Yahuza, Isra'ila kuwa za ta zauna lafiya. Sunan da za a kira shi da shi ke nan, ‘Ubangiji Adalcinmu.’


Don haka zan yabe ka a cikin al'ummai, Zan raira maka yabo.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.


Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ