Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Filibbiyawa 1:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Filibbiyawa 1:5
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don kuwa mun zama masu tarayya da Almasihu, muddin muna tsaye da ƙarfi a kan amincewar nan tamu ta fari, har zuwa ƙarshe.


Saboda haka in ka ɗauke ni a kan abokin tarayya, to, sai ka karɓe shi kamar yadda za ka karɓe ni.


Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.


to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyar nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu.


wato, yadda ta wurin bishara al'ummai da suke abokan gādo da mu, gaɓoɓin jiki guda, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Almasihu Yesu.


To, 'yan'uwa, muna so mu sanar da ku alherin Allah da ya bayar a cikin ikilisiyoyin Makidoniya,


Mutanen Makidoniya da na Akaya, sun ji daɗin yin gudunmawar daidai gwargwado ga matalauta, a cikin tsarkakan da suke a Urushalima.


In kuwa muna zaune a haske, kamar yadda shi yake cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.


Daga Saminu Bitrus, bawan Yesu Almasihu, manzonsa kuma, zuwa ga waɗanda aka yi wa baiwar bangaskiya mai daraja iri ɗaya da tamu, albarkacin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Almasihu.


Saboda haka, ya ƙaunatattuna, kamar yadda a kullum kuke biyayya, haka kuma yanzu, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba ma sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan.


Allah mai alkawari ne, shi ne kuma ya kira ku ga tarayya da Ɗansa Yesu Almasihu Ubangijinmu.


Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni'imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,


Sai suka himmantu ga koyarwar manzanni da tarayya da juna, da gutsuttsura gurasa, da kuma yin addu'a.


Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.


'Yan'uwa, ina so ku sani, al'amuran nan da suka auku a gare ni, har ma sun yi amfani wajen yaɗa bishara,


Waɗannan suna yi ne a kan ƙauna, sun sani, an sa ni nan ne domin kāriyar bishara.


Sai dai ku yi zaman da ya cancanci bisharar Almasihu, domin ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku, cewa kun dage, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyar da bishara take sawa,


Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.


Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka, ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni a al'amarin bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a cikin Littafin Rai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ