Don ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan tare da ku, ina kuwa farin cikin ganin kyakkyawan tsarinku, da dagewarku a kan bangaskiyarku ga Almasihu.
Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.
Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”