An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.
Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata.
Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”
Amma ni ko kusa ba zan yi fariya ba, sai dai a game da gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta albarkacin mutuwarsa a kan gicciye ne na yar da sha'anin duniya, duniya kuma ta yar da sha'anina.
Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.