Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Filibbiyawa 1:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Har ma galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka ƙarfafa saboda ɗaurina, sun kuma ƙara fitowa gabagaɗi, su faɗi Maganar Allah ba tare da tsoro ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Saboda sarƙoƙina, yawancin ’yan’uwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagadi da kuma babu tsoro.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Filibbiyawa 1:14
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.


Domin yana cetonmu daga abokan gābanmu, Mu bauta masa ba da jin tsoro ba,


domin in bayyana shi sosai, kamar yadda ya kamata in faɗa.


Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.


Tikikus zai sanar da ku duk abin da nake ciki. Shi ƙaunataccen ɗan'uwa ne, amintaccen mai hidima, abokin bautarmu kuma a cikin Ubangiji.


Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.


Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.


Tun da yake muna da sa zuciya irin wannan, to, muna magana ne gabanmu gaɗi ƙwarai.


Na amince da ku ƙwarai, ina kuma taƙama da ku gaya. Zuciyata ta ƙarfafa ƙwarai. Duk da wahalce-wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.


Don kuwa ina ɗoki, ina kuma sa zuciya, ko kaɗan ba zan kunyata ba, sai dai zan yi ƙarfin hali matuƙa a yanzu kamar koyaushe, a girmama Almasihu a jikina, ko ta wurin rayuwata, ko ta wurin mutuwata.


wadda nake shan wuya saboda ita, har nake ɗaure kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a ɗaure take ba.


Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Fito nan fili.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ