9 “Ga shi, na kafa alkawari tsakanina da ku da zuriyarku a bayanku,
9 “Yanzu na kafa alkawarina da ku da zuriyarku a bayanku,
Amma ni zan kafa alkawari tsakanina da kai, za ka shiga cikin jirgin, kai da 'ya'yanka, da matarka, da matan 'ya'yanka tare da kai.
Bishara ɗin nan a kan Ɗansa ce, Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ga jiki shi zuriyar Dawuda ne,
Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawari wanda na kafa tsakanina da dukan talikan da suke bisa duniya.”
Na kafa alkawarina da ku. Daɗai ba za a ƙara hallaka talikai duka da ruwa ba, ba kuma za a ƙara yin Ruwan Tsufana da zai hallaka duniya ba.”
idan ka iya hana dare da yini su bayyana a ƙayyadaddun lokatansu,
hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,
Allah kuwa ya ce wa Nuhu da 'ya'yansa.
da kowane mai rai da yake tare da ku, da tsuntsaye, da dabbobin gida da na jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin, kowane mai rai na duniya.