29 Shekarun Nuhu duka ɗari tara da hamsin ne, ya rasu.
29 Gaba ɗaya dai, Nuhu ya yi shekara 950, sa’an nan ya mutu.
Sa'ad da Nuhu ya yi shekara ɗari biyar, ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.
Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu.
Tsawon kwanakin ranmu duka a ƙalla shekara ce saba'in, In kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne. Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaru Suke kawo mana, damuwa ce da wahala, Nan da nan sukan wuce, Tamu da ƙare.
Haka nan kuwa dukan kwanakin Yared shekara ce ɗari tara da sittin da biyu, ya rasu.
Haka nan kuwa dukan kwanakin Adamu shekara ce ɗari tara da talatin, ya rasu.
Bayan Ruwan Tsufana, Nuhu ya yi shekara ɗari uku da hamsin.
Waɗannan su ne zuriyar 'ya'yan Nuhu, da Shem, da Ham, da Yafet. Bayan Ruwan Tsufana sai aka haifa musu 'ya'ya.