Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 9:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahna, ya sa wa Shem albarka, Kan'ana kuwa ya bauta masa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Ya kuma ce, “Albarka ta tabbata ga Ubangiji Allah na Shem! Bari Kan’ana yă zama bawan Shem.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 9:26
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mai farin ciki ce al'ummar Da abin nan da aka faɗa ya zama gaskiya a gare ta. Masu farin ciki ne jama'ar da Allahnsu shi ne Ubangiji!


Amma bisa ga hakika sun ɗokanta ne a kan wata ƙasa mafi kyau, wato ta Sama. Saboda haka ne, Allah ba ya jin kunya a ce da shi Allahnsu, don kuwa ya shirya musu birni.


Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo yā tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome. Amin.


“Babu wani kamar Allahn Yeshurun, Wanda yakan sauko daga Sama don ya cece ka, Wanda ya sauko daga bisa da ɗaukakarsa.


Ishaku ya amsa wa Isuwa ya ce, “Ga shi, na shugabantar da shi a kanka da dukan 'yan'uwansa na ba shi su, su zama barorinsa, na ba shi hatsi da ruwan inabi. Me zan yi maka kuma, ya ɗana?”


Ta wurin takobinka za ka rayu Za ka yi wa ɗan'uwanka barantaka, Amma sa'ad da ka ɓalle, Za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.”


Ga Allah Maɗaukaki yabo ya tabbata, shi wanda ya ba ka maƙiyanka a tafin hannunka!” Abram kuwa ya ba shi ushiri na duka.


ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga maigidana ba. Ubangiji ya bi da ni har zuwa gidan ɗan'uwan maigidana.”


Bari jama'a su bauta maka, Al'ummai kuma su sunkuya maka. Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka, Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka su sunkuya maka. La'ananne ne dukan wanda ya la'anta ka, Albarkatacce ne dukan wanda ya sa maka albarka.”


Yanzu fa ku la'anannu ne, a cikinku ba za a rasa bayin da za su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin masujadar Allahnmu ba.”


Sa'ad da Isra'ilawa suka yi ƙarfi, suka sa Kan'aniyawa su yi aikin gandu, amma ba su kore su ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ