Amma Joshuwa ya sa su su zama masu saro itace da masu ɗebo ruwa domin jama'a da bagaden Ubangiji. Zai zama aikinsu na yau da kullum a wurin da Ubangiji zai zaɓa.
La'ananne ne fushinsu domin mai tsanani ne, Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce. Zan warwatsa su cikin dukan ƙasar Yakubu, In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa.
Ubangiji Allah ya ce wa maciji, “Tun da ka aikata wannan, za a hukunta ka. Kai kaɗai wannan la'ana za ta bi. Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya, turɓaya za ka ci muddin rayuwarka.