20 Nuhu shi ya fara noma, ya yi gonar inabi.
20 Nuhu, mutumin ƙasa, shi ne farko da ya fara yin gonar inabi.
Abin da ƙasa take bukata, shi ne sarkin da yake kulawa da aikin gona.
Na ratsa ta gonakin inabin wani malalaci, dakiki,
Manomin da yake aiki ƙwarai yana da isasshen abinci. Wauta ce a ɓatar da lokaci a kan aikin banza.
Kalmomin mutumin kirki maɓuɓɓugan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.
“Za ku yi tashin yarinya, wani ne zai kwana da ita. Za ku gina gida, wani ne zai zauna a ciki. Za ku dasa inabinku, wani ne zai girbe amfanin.
Ko akwai wani mutum wanda ya dasa gonar inabi da bai ci amfaninta ba? Sai ya koma gidansa, kada ya mutu a yaƙi, wani dabam ya ci amfaninta.
ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la'anta.”
Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne.
Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato inda aka ɗauko shi.
Wa yake yin aikin soja, sa'an nan yă ci da kansa? Wa zai shuka garkar inabi, yă kasa cin 'ya'yan? Wa zai yi kiwon garke, yă kasa shan nonon?
Kada ka raina ni saboda launina, Domin rana ta dafe ni. 'Yan'uwana suna fushi da ni, Sun sa ni aiki a gonar inabi. Ba ni da zarafin da zan lura da kaina.
Su uku ɗin nan su ne 'ya'yan Nuhu, daga gare su duniya za ta cika da mutane.
Ya sha daga cikin ruwan inabin ya kuwa bugu, ya kwanta tsirara a cikin alfarwarsa.