Farawa 9:15 - Littafi Mai Tsarki15 zan tuna da alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da dukan talikai. Ruwa kuma ba zai ƙara yin rigyawar da za ta hallaka talikai duka ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 zan tuna da alkawari tsakanina da ku da kuma dukan halittu masu rai na kowane iri. Ruwa ba zai sāke yin ambaliyar da za tă hallaka dukan masu rai ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.