Ya kurciyata kina zaune a kogon dutse mai tsayi. Bari in ga fuskarki, in kuma ji muryarki, Gama muryarki tana da daɗin ji, Fuskarki kuma tana da kyan gani.
amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi.