wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa'ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa.
Ka fito da kowane abu mai rai tare da kai, dukan talikai, wato tsuntsaye, da dabbobi, da kowane abu mai rarrafen da yake rarrafe bisa ƙasa, domin su hayayyafa su kuma riɓaɓɓanya a duniya.”
da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abin da yake motsi a bisa duniya, suka fito daga jirgi ɗaki ɗaki bisa ga irinsu.
Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi.