Gama firistocin da suke ɗauke da akwatin sun tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Joshuwa ya faɗa wa jama'a, da kuma bisa ga dukan abin da Musa ya umarce shi. Mutanen kuwa suka gaggauta, suka haye.
A sa'ad da Isra'ilawa duka suna tafiya a kan sandararriyar ƙasa a cikin Urdun, firistoci kuwa waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari na Ubangiji suka yi ta tsayawa a bisa sandararriyar ƙasa a tsakiyar Urdun har al'ummar ta gama hayewa.
Ka fito da kowane abu mai rai tare da kai, dukan talikai, wato tsuntsaye, da dabbobi, da kowane abu mai rarrafen da yake rarrafe bisa ƙasa, domin su hayayyafa su kuma riɓaɓɓanya a duniya.”