A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.
A rana ta fari ga wata na fari na shekara ta ɗari shida da ɗaya na Nuhu, ruwa ya ƙafe a duniya. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya duba, sai ga ƙasa busasshiya.
A rana ta ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu, a shekara ta talatin da bakwai ta ɗaurin Yekoniya Sarkin Yahuda, sai Ewil-merodak da ya zama Sarkin Babila ya yi wa Yekoniya alheri, ya sake shi a shekarar da ya ci sarautar.