5 Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.
5 Nuhu ya aikata duk abin da Ubangiji ya umarce shi.
Nuhu ya yi dukan abin da Allah ya umarce shi.
Amma ya amsa musu ya ce, “Masu jin Maganar Allah, suna kuma aikata ta, ai, su ne uwata, su ne kuma 'yan'uwana.”
Idan na kula da dukan umarnanka, To, ba zan kasa kaiwa ga burina ba.
Haka kuwa aka gama dukan aiki na alfarwa ta sujada. Isra'ilawa suka yi shi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Ko da yake shi Ɗa ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha,
Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta wurin yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta gicciye.
In dai kun san wannan, kuna kuma aikatawa, ku masu farin ciki ne.
Amma Yesu ya amsa masa ya ce, “Bari ya zama haka a yanzu, domin haka ne ya dace mu cika dukan adalci.” Sa'an nan Yahaya ya yardar masa.
Haka kuwa Musa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.
Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.”
Musa da Haruna suka yi yadda Ubangiji ya umarce su.