Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 7:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Aka kawar da kowane abu mai rai, mutane da dabbobi da halittu masu rarrafe a ƙasa, da tsuntsayen sama a doron ƙasa, duka aka kawar da su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 7:23
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,


wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa'ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa.


Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.


Ta haka ne kuma, duniyar wancan zamani, ruwa ya sha kanta, ta hallaka.


Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”


ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari'a,


Dukiya ba ta da wani amfani a ranar mutuwa, amma adalci zai hana ka mutuwa.


Duk wanda ya je wurin Maɗaukaki Zai zauna lafiya, Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka,


Yakan tsare ka daga cuta sau shida har sau bakwai, Ba muguntar da za ta taɓa ka.


Mutum dubu za su fāɗi daura da kai, Dubu goma kuma za su fāɗi dama da kai, Amma kai, ba za a cuce ka ba.


Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu.


Sai Nuhu ya fito, da 'ya'yansa, da matarsa da matan 'ya'yansa tare da shi,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ