Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 7:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Kowane abu mai rai da yake tafiya a duniya ya hallaka, tsuntsaye, dabbobin gida, namun jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe a duniya, da kuma dukan mutane.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 7:21
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.


Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba'in da dare arba'in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya.”


Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu.


An sarayar da halitta ta zama banza, ba da nufinta ba, amma da nufin wanda ya sarayar da ita. Duk da haka, akwai sa zuciya,


tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,


Mun dai san dukan halitta tana nishi, na shan azaba kuma irin ta mai naƙuda, har ya zuwa yanzu.


Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, Ruwan Tsufana kuma ya zo, ya hallaka su duka.


ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.


Zan shafe mutum da dabba, Zan shafe tsuntsayen sararin sama da kifayen teku, Zan kuma rushe gumakansu tare da mugaye, Zan kuma datse ɗan adam daga duniya.


Tana cinye shuke-shuke kamar wuta, Ƙasa kamar gonar Adnin take kafin ta zo, Amma a bayanta ta zama hamada, Ba abin da ya tsere mata.


Saboda haka ƙasar za ta yi makoki, Dukan waɗanda yake zaune a cikinta za su yi yaushi. Namomin jeji kuma, da tsuntsaye, da kifaye za su ƙare.


Saboda haka Allah ya aiko da la'ana ta hallaka duniya. Jama'arta suna karɓar sakayyar abin da suka aikata. 'Yan kalilan ne suka ragu da rai.


Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.


Da duk mai rai ya halaka, Mutum kuma ya koma ƙura.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ