Sa'ad da mala'ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima don ya hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala'ikan da yake hallakar da mutanen, “Ya isa, ka janye hannunka.” Mala'ikan ya tsaya kusa da masussukar Arauna Bayebuse.
Ku kyakkece zuciyarku, ba tufafinku kaɗai ba.” Ku komo wurin Ubangiji Allahnku. Gama shi mai alheri ne, mai jinƙai, Mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, Yakan tsai da hukunci.
Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’
Ashe, Hezekiya Sarkin Yahuza da dukan Yahuza sun kashe shi ne? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji, ya roƙi alherinsa ba? Ashe, Ubangiji bai janye masifar da ya hurta a kansu ba? Yanzu fa gab muke da mu jawo wa kanmu babbar masifa.”
Allah ya aiko mala'ikansa don ya hallaka Urushalima, amma sa'ad da yake gab da hallaka ta, sai Ubangiji ya gani, ya janye shirin annobar, ya ce wa mala'ikan hallakarwa, “Ya isa, janye hannunka.” Mala'ikan Ubangiji kuwa na tsaye kusa da masussukar Arauna Bayebuse.
“Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum! Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominku Kamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba! Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwa Da suke bugowa zuwa gāɓa.
Daga ran nan Sama'ila bai ƙara saduwa da sarki Saul ba, har rasuwar Sama'ila, amma ya ji juyayin Saul. Ubangiji kuwa bai ji daɗi da ya sa Saul ya zama Sarkin Isra'ila ba.
Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
“Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu? Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma? Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim? Zuciyata tana motsawa a cikina, Juyayina ya huru.