10 Nuhu kuwa ya haifi 'ya'ya uku, Shem, da Ham, da Yafet.
10 Nuhu yana da ’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
Sa'ad da Nuhu ya yi shekara ɗari biyar, ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.
Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah.
Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko'ina.