Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 50:17 - Littafi Mai Tsarki

17 ya ce, ‘Ku faɗa wa Yusufu, ina roƙonsa, ya gafarta laifin 'yan'uwansa da zunubansu, gama sun yi masa mugunta.’ Yanzu fa, muna roƙonka, ka gafarta laifofin bayin Allah na mahaifinka.” Yusufu ya yi kuka sa'ad da suka yi magana da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ga abin da za ku ce wa Yusuf, ‘Na roƙe ka, ka gafarta wa ’yan’uwanka zunubai da laifofin da suka aikata na abubuwa marasa kyau da suka yi maka.’ Yanzu muna roƙonka ka gafarta zunuban bayin Allah na mahaifinka.” Sa’ad da saƙonsu ya zo masa, sai Yusuf ya yi kuka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 50:17
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe muku ta wurin Almasihu.


Ba za ka taɓa cin nasara a zamanka ba muddin kana ɓoye laifofinka. Ka hurta zunubanka ka tuba, sa'an nan Allah zai yi maka jinƙai.


Sun ƙulla mugayen dabaru, suna fakonsa, Amma ba za su yi nasara ba.


Ta wurin Allah na mahaifinka wanda zai taimake ka, Ta wurin Allah Mai Iko Dukka wanda zai sa maka albarka Albarkun ruwan sama daga bisa, Da na zurfafa daga ƙarƙashin ƙasa, Da albarkun mama da na mahaifa.


Don haka, ba ku kuka aiko ni nan ba, amma Allah ne, shi ne kuwa ya sa in zama uba ga Fir'auna, da shugaban gidansa duka, mai mulki kuma bisa ƙasar Masar duka.


Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.


Salama da jinƙai su tabbata ga duk masu bin ka'idar nan, wato Isra'ilar gaske ta Allah.


To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda suke jama'ar masu ba da gaskiya ba.


Da almajiran nan goma suka ji haka, suka fara jin haushin Yakubu da Yahaya.


Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’


Haka kuma Ubana da yake Sama zai yi da ko wannenku, in ba ku yafe wa 'yan'uwanku da zuciya ɗaya ba.”


Kowa ya ba ɗaya daga cikin 'yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”


Ka gafarta mana laifofinmu, Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.


A nufinku mugunta ce kuka yi mini, amma Allah ya maishe ta alheri, don a rayar da jama'a masu yawa waɗanda suke da rai a yau.


Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”


Saboda haka suka aika wa Yusufu da jawabi, suka ce, “Mahaifinka ya ba da wannan umarni kafin rasuwarsa,


'Yan'uwansa kuma suka zo suka fāɗi a gabansa, suka ce, “Ga shi, mu barorinka ne.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ