Sa'ad da Ka'aniyawa mazaunan ƙasar, suka ga makokin da aka yi a farfajiyar masussukar Atad, sai suka ce, “Wannan makoki mai zafi ne ga Masarawa.” Don haka aka sa wa wurin suna Abel-mizrayim, wanda yake wajen Urdun.
gama 'ya'yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan'ana, suka kuwa binne shi a kogon da yake saurar Makfela a gabashin Mamre, wanda Ibrahim ya saya, duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.