Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 5:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 5:3
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai kuma Adamu ya san matarsa, ta kuwa haifi ɗa, ta raɗa masa suna Shitu, gama ta ce, “Allah ya arzuta ni da ɗa maimakon Habila wanda Kayinu ya kashe.”


Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam.


Don ba dukan tsoka ce iri ɗaya ba, mutane da irin tasu, dabbobi ma da irin tasu, tsuntsaye da irin tasu, kifaye kuma da irin tasu.


To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gādo ga kowa, don kowa ya yi zunubi.


Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne.


Mala'ikan ya amsa mata ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki. Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.


Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni, Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.


Akwai wanda ya isa ya zama adali, Ko mai tsarki a gaban Allah?


Ba wani abu tsarkakakke Da zai fito daga cikin kowane marar tsarki, kamar mutum.


Shela ɗan Kenan, Kenan ɗan Arfakshad, Arfakshad ɗan Shem, Shem ɗan Nuhu, Nuhu ɗan Lamek,


Kamar yadda muka ɗauki siffar na turɓayar nan, haka kuma za mu ɗauki siffar na Saman nan.


Namiji da ta mace ya halicce su, ya sa musu albarka, ya sa musu suna, Mutum, sa'ad da aka halicce su.


Bayan da Adamu ya haifi ɗansa Shitu, ya yi shekara ɗari takwas, sa'an nan ya haifi 'ya'ya mata da maza.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ