Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 5:29 - Littafi Mai Tsarki

29 ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la'anta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 5:29
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

tun da yake bai rangwanta wa mutanen tun can dā dā kuma ba, amma ya kiyaye Nuhu mai wa'azin adalci, da waɗansu mutum bakwai, sa'ad da ya aiko da Ruwan Tsufana zuwa a cikin duniyar nan ta marasa bin Allah,


Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.


Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.


ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu.


ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu, ni Ubangiji na faɗa.


“Na yi alkawari a zamanin Nuhu, Cewa ba zan ƙara rufe duniya da Ruwan Tsufana ba. Yanzu kuwa ina miki alkawari, Cewa ba zan ƙara yin fushi da ke ba, Ba zan ƙara tsawata miki, ko in hukunta ki ba.


Sa'ad da ruwan inabin ya sau Nuhu, ya san abin da ƙaramin ɗansa ya yi masa.


wato, waɗanda dā ba su bi ba, sa'ad da Allah ya yi jira da haƙuri a zamanin Nuhu, a lokacin sassaƙar jirgin nan, wanda a cikinsa mutane kaɗan, wato takwas suka kuɓuta ta ruwa.


Shela ɗan Kenan, Kenan ɗan Arfakshad, Arfakshad ɗan Shem, Shem ɗan Nuhu, Nuhu ɗan Lamek,


Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi.


An sarayar da halitta ta zama banza, ba da nufinta ba, amma da nufin wanda ya sarayar da ita. Duk da haka, akwai sa zuciya,


Sa'ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa,


Bayan da Lamek ya haifi Nuhu ya yi shekara ɗari biyar da tasa'in da biyar, ya haifi 'ya'ya mata da maza.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ