27 Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu.
27 Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu.
Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza.
Sa'ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa,
Shekarun Nuhu duka ɗari tara da hamsin ne, ya rasu.
Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.”
Barzillai kuwa tsoho ne, yana da shekara tamanin. Ya taimaki sarki da abinci sa'ad da sarki yake a Mahanayim, gama shi attajiri ne.