25 Sa'ad da Metusela ya yi shekara ɗari da tamanin da bakwai, ya haifi Lamek.
25 Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek.
An haifa wa Anuhu ɗa, wato Airad. Airad ya haifi Mehuyayel, Mehuyayel kuwa ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifi Lamek.
Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba.
Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi 'ya'ya mata da maza.