Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 49:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Yahuza ɗan zaki ne, Ya kashe ganima sa'an nan ya komo wurin ɓuyarsa. Yahuza kamar zaki yake, Yakan kwanta a miƙe, Ba mai ƙarfin halin da zai tsokane shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda, ka dawo daga farauta, ɗana. Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe, kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 49:9
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Al'ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zaki Sa'ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi. Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka, Duk wanda ya sa muku la'ana zai sami la'ana.”


Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce mini, “Kada ka yi kuka. Ga shi, Zakin nan na kabilar Yahuza, Tsatson Dawuda, ya ci nasara har yake da iko yă buɗe littafin nan da hatimansa bakwai.”


Ga shi, jama'ar Isra'ila tana kama da ƙaƙƙarfan zaki, Ba zai kwanta ba sai ya cinye ganimarsa. Ya lashe jinin waɗanda ya kashe.”


Ringin Yakubu kuma zai zamar wa al'umman duniya, Kamar yadda zaki yake a tsakanin namomin jeji, Kamar kuma yadda zaki yake a tsakanin garkunan tumaki, Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakan tattaka, Ya yi kacakaca da su, Ba wanda zai cece su.


Zan zama kamar zaki ga Ifraimu, Kamar sagarin zaki ga mutanen Yahuza. Ni kaina zan yayyage, in yi tafiyata. Zan ɗauka, in tafi, ba wanda zai yi ceto.”


Sa'ad da ta ga wanda ta sa zuciya a kansa ya tafi, Sai ta ɗauki ɗaya kuma daga cikin kwiyakwiyanta, Ta goye shi ya zama sagari.


Sa'an nan sai ƙarshen, sa'ad da zai mayar wa Allah Uba mulki, bayan ya shafe dukkan sarauta da mulki da iko.


“Ayyukansu ba su bar su Su koma wurin Allahnsu ba, Gama halin karuwanci yana cikinsu, Don haka kuma ba su san Ubangiji ba.


A kan Gad, ya ce, “Mai albarka ne wanda ya fāɗaɗa Gad, Gad yana sanɗa kamar zaki, Yana yayyage hannu da ƙoƙon kai.


Akwai siffar zaki goma sha biyu suna tsaye a kowane gefen matakan nan shida. Ba a taɓa yin irinsu a kowace masarauta ba.


Gadon sarautar yana da matakai da 'yar kujerar zinariya ta ɗora ƙafa haɗe da gadon. A kowane gefen gadon an yi wurin ɗora hannu, akwai kuma siffar zaki a tsaye kusa da kowane wurin ɗora hannun.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ