Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 49:8 - Littafi Mai Tsarki

8 “Yahuza, 'yan'uwanka za su yabe ka, Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka, 'Yan'uwanka za su rusuna a gabanka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 “Yahuda, ’yan’uwanka za su yabe ka; hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka, ’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 49:8
38 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Tabbatacce ne, cewa Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuza ne, Musa kuwa bai ce kome ba a game da kabilar nan a kan zancen firistoci.


Bari jama'a su bauta maka, Al'ummai kuma su sunkuya maka. Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka, Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka su sunkuya maka. La'ananne ne dukan wanda ya la'anta ka, Albarkatacce ne dukan wanda ya sa maka albarka.”


Ko da yake Yahuza ya rinjayi 'yan'uwansa, har daga gare shi aka sami shugaba, duk da haka matsayin ɗan farin na Yusufu ne.


Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra'ilawa, sa'an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu.


A kan Yahuza ya ce, “Ka ji muryar Yahuza, ya Ubangiji, Ka kawo shi wurin jama'arsa. Ka yi yaƙi da ikonka dominsu, Ka taimake shi a kan maƙiyansa.”


Har yanzu kuwa ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta raɗa masa suna Yahuza. Daga nan sai ta daina haihuwa.


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce mini, “Kada ka yi kuka. Ga shi, Zakin nan na kabilar Yahuza, Tsatson Dawuda, ya ci nasara har yake da iko yă buɗe littafin nan da hatimansa bakwai.”


tun daga lokacin nan yana jira, sai an sa ya take maƙiyansa.


“ ‘Ka faɗa wa Ammonawa, cewa wahayin da suke gani ƙarya ne annabcin da suke yi kuma ƙarya ne. Su mugaye ne, ranar hukuncinsu tana zuwa. Za a sare wuyansu da takobi.


Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.


Allah sananne ne a Yahuza, Mashahuri ne kuma a Isra'ila.


Sai mutane kaɗan na Ashiru, da na Manassa, da na Zabaluna suka yi tawali'u, suka zo Urushalima.


Ya sa sojoji a kowane birni mai kagara a Yahuza, ya kuma sa ƙungiyoyin sojoji masu tsaro a ƙasar Yahuza, da kuma a biranen Ifraimu waɗanda tsohonsa Asa ya ci da yaƙi.


Sai ya tattara dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, da kuma na Ifraimu, da na Manassa, da na Saminu, waɗanda suke zaman baƙunci tare da su. Da yawa daga cikin Isra'ilawa suka yi ƙaura zuwa wurinsa, sa'ad da suka ga Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.


Sarki Asa kuwa yana da soja dubu ɗari uku (300,000) a Yahuza, ko wanne yana da kutufani da māshi, yana da soja dubu ɗari biyu da dubu tamanin (280,000) daga Biliyaminu, 'yan baka ko wanne da garkuwarsa. Dukansu manyan jarumawa ne.


Yowab kuwa ya ba sarki yawan jimillar mutanen da aka samu. A Isra'ila an sami mutanen da suka isa yin yaƙi, su dubu ɗari takwas (800,000). A Yahuza kuwa an sami mutum dubu ɗari biyar (500,000).


Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana, Na hallaka waɗanda suke ƙina.


Sai dukan dattawan Isra'ila suka tafi wurin sarki Dawuda a Hebron, shi kuwa ya yi alkawari da su a gaban Ubangiji. Su kuwa suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka.


Isra'ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?” Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.”


Waɗannan su ne iyalan kabilar Yahuza. Yawan mutanensu ya kai dubu saba'in da shida da ɗari biyar (76,500).


Tutar zangon kabilar mutanen Yahuza ta fara tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Nashon, ɗan Amminadab, shi ne shugaban rundunarsu.


'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.


Yanzu fa, Yusufu shi ne mai mulkin ƙasar, shi ne kuwa mai sayar wa jama'ar ƙasar duka. 'Yan'uwan Yusufu suka zo suka sunkuya har ƙasa a gabansa.


Sauran 'ya'yansa bisa ga iyalansu su ne, Shela, da Feresa, da Zera,


Duk da haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya zaɓe ni da zuriyata daga cikin gidan mahaifina, in zama Sarkin Isra'ilawa har abada. Gama shi ya zaɓi Yahuza ya zama shugaba. Daga cikin gidan Yahuza kakana, da kuma daga cikin 'ya'yan mahaifina, maza, ya ji daɗina har ya naɗa ni sarkin dukan Isra'ila.


Wannan shi ne gādon jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ