Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 49:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba, Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsu ba, Gama cikin fushinsu suka kashe mutane, Cikin gangancinsu kuma suka gurgunta bijimai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ba zan shiga shawararsu ba, ba zan shiga taronsu ba, gama sun kashe maza cikin fushinsu cikin ganin dama suka kashe bijimai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 49:6
29 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Yakubu ya ce wa Saminu da Lawi, “Kun jawo mini wahala. Kun sa na zama abin ƙi ga Kan'aniyawa da Ferizziyawa mazaunan ƙasar. Mutanena kima ne, in suka haɗa kai suka fāɗa mini, za su hallaka ni, da ni da gidana.”


Kada ka hallaka ni tare da masu zunubi, Ka cece ni daga ƙaddarar masu kisankai,


Don haka cike nake da murna da farin ciki, Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake,


Kada ku yi cuɗanya marar dacewa da marasa ba da gaskiya. To, me ya haɗa aikin adalci da na mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?


Zan kuma ce wa raina, “Lalle ina da kaya masu yawa a jibge, tanadin shekara da shekaru. Bari in huta, in yi ta ci, in yi ta sha, ina shagali.” ’


Ban zauna cikin ƙungiyar masu annashuwa ba. Ban kuwa yi murna ba, Na zauna ni kaɗai saboda kana tare da ni, Gama ka sa na cika da haushi.


Azaba! Ba zan iya daurewa da azaba ba! Zuciyata! Gabana yana faɗuwa da ƙarfi, Ba zan iya yin shiru ba, Gama na ji amon ƙaho da hargowar yaƙi.


Ka kiyaye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, Da iskancin mugayen mutane.


Ka farka, ya raina! Ku farka, molona da garayata! Zan sa rana ta farka!


Amintattun mutane za su yi maka abin da yake daidai, amma mugaye za su ruɗe ka.


in suka ce maka, “Zo mu tafi mu nemi wani mutum mu kashe, mu je, mu fāɗa wa marasa laifi mu ji daɗi!


Ya Allah, da yadda nake so ne, da sai ka karkashe mugaye! 'Yan ta da zaune tsaye kuma sai su rabu da ni!


Ka yabi Ubangiji, ya raina! Ka yabi sunansa mai tsarki!


Me ya sa nake baƙin ciki? Me ya sa nake damuwa? Zan dogara ga Allah, Zan ƙara yabonsa, Mai Cetona, Allahna.


Me ya sa ni ɓacin rai haka? Me ya sa ni damuwa? Zan dogara ga Allah. Har yanzu ma zan yabe shi, Mai Cetona, Allahna.


Me ya sa nake baƙin ciki haka? Me ya sa nake damuwa ƙwarai? Zan dogara ga Allah, Zan sāke yin yabonsa, Mai Cetona, Allahna.


Don haka ba zan yi shiru ba, Zan raira maka yabo, Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan gode maka har abada.


Kada ka kāshe ni tare da mugaye, Tare da masu aikata mugunta, Mutane waɗanda maganarsu kamar ta zumunci ce, Amma zukatansu cike suke da ƙiyayya.


Ka kāshe su, ka hukunta su, ya Allah Ka watsar da mugayen shirye-shiryensu, Ka kore su daga gabanka sabili da yawan zunubansu, Da kuma tayarwar da suke yi maka.


Albarka ta tabbata ga mutumin da Ba ya karɓar shawarar mugaye, Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi, Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.


Ambaliyar Kishon ta kwashe su, Wato tsohon Kogin Kishon. Zan yi gaba, in yi gaba da ƙarfi!


“ ‘La'ananne ne wanda ya buge maƙwabcinsa daga ɓoye.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’


Joshuwa kuwa ya yi musu kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, ya daddatse agaran dawakansu, ya kuma ƙone karusansu.


Dawuda ya ƙwace masa mahayan dawakai dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), da sojojin ƙafa dubu ashirin (20,000). Dawuda ya yanyanke agarar dawakan, sai dai doki ɗari ne ya bari.


Sai Dawuda ya ƙwace karusai dubu (1,000), da mahayan dawakai dubu bakwai (7,000), da sojojin ƙasa dubu ashirin (20,000) daga gare shi. Dawuda kuma ya yanyanke agarar dawakan da suke jan karusai, amma ya bar waɗansu dawakai daga cikinsu waɗanda suka isa jan karusai ɗari.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ