Farawa 49:3 - Littafi Mai Tsarki3 “Ra'ubainu, kai ɗan farina ne, ƙarfina, Ɗan balagata, isasshe kuma, mafi ƙarfi duka cikin 'ya'yana. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 “Ruben, kai ne ɗan farina, ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina, mafi matsayi, kuma mafi iko. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Mazaje masu shekara ashirin ko fi da suka isa yaƙi aka rubuta su suna suna, bisa ga kabilansu da iyalansu, aka fara da kabilar Ra'ubainu, babban ɗan Yakubu. Ga yadda jimillarsu take. Kabila Jimilla Ra'ubainu (46,500) Dubu arba'in da shida da ɗari biyar. Saminu (59,300) Dubu hamsin da tara da ɗari uku. Gad (45,650) Dubu arba'in da biyar da ɗari shida da hamsin. Yahuza (74,600) Dubu saba'in da huɗu da ɗari shida. Issaka (54,400) Dubu hamsin da huɗu da ɗari huɗu. Zabaluna (57,400) Dubu hamsin da bakwai da ɗari huɗu. Ifraimu (40,500) Dubu arba'in da ɗari biyar. Manassa (32,200) Dubu talatin da biyu da ɗari biyu. Biliyaminu (35,400) Dubu talatin da biyar da ɗari huɗu. Dan (62,700) Dubu sittin da biyu da ɗari bakwai. Ashiru (41,500) Dubu arba'in da ɗaya da ɗari biyar. Naftali (53,400) Dubu hamsin da uku da ɗari huɗu. Jimilla duka (603,550) dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin.