Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 49:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama'ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 49:29
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

gama 'ya'yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan'ana, suka kuwa binne shi a kogon da yake saurar Makfela a gabashin Mamre, wanda Ibrahim ya saya, duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.


amma bari in kwanta tare da kakannina, ka ɗauke ni daga Masar, ka binne ni a makabartarsu.” Ya amsa ya ce, “Zan aikata yadda ka faɗa.”


Kai kuwa, cikin salama za ka koma ga iyayenka, da kyakkyawan tsufa za a binne ka.


Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu suke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala.


Ina roƙonka ka bar ni in koma domin in rasu a garinmu, kusa da kabarin mahaifina. Amma ga Kimham barana, bari ya tafi tare da kai, ranka ya daɗe. Ka yi masa yadda kake so.”


Sai Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya rasu, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi, da kyakkyawan tsufa cike da kwanaki, 'ya'yansa Isuwa da Yakubu suka binne shi.


Ibrahim ya yarda da Efron. Ibrahim kuwa ya auna wa Efron yawan shekel da ya ambata a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu bisa ga nauyin da 'yan kasuwa suke amfani da shi a wancan lokaci.


Don haka saurar Efron da yake cikin Makfela wadda take gabashin Mamre, da saurar, da kogon da yake ciki, da dukan itatuwan da suke cikin saurar, iyakar girmanta duka


Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa kowannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.


Sa'ad da Yakubu ya gama yi wa 'ya'yansa maza wasiyya, sai ya hau da ƙafafunsa bisa kan gado, Ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi.


ya ba ni kogon Makfela nasa na can ƙarshen saurarsa. Bari ya sallama mini wurin a gabanku a cikakken kuɗinsa, ya zama mallakata domin makabarta.”


Da saurar, da kogon da yake cikinta, aka tabbatar wa Ibrahim mallakarsa ce don makabarta da iznin Hittiyawa.


Yakubu kuma ya zo wurin mahaifinsa a Mamre, a Kiriyat-arba, wato Hebron ke nan, inda Ibrahim da Ishaku suka yi baƙunci.


Haka 'ya'yansa suka yi masa kamar yadda ya umarta,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ