Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 49:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Ta wurin Allah na mahaifinka wanda zai taimake ka, Ta wurin Allah Mai Iko Dukka wanda zai sa maka albarka Albarkun ruwan sama daga bisa, Da na zurfafa daga ƙarƙashin ƙasa, Da albarkun mama da na mahaifa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka, saboda Maɗaukaki, wanda yake albarkace ka da albarkar sama da take bisa albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa albarkun mama da kuma mahaifa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 49:25
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka hayayyafa ka riɓaɓɓanya, al'umma da tattaruwar al'ummai za su bumbunto daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka.


Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka.


Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku daga cikin yalwar ɗaukakarsa da take ga Almasihu Yesu.


Kada ku ce a zuciya, ‘Ai, ikona da ƙarfin hannuwana ne suka kawo mini wannan wadata.’


Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba.


Wannan ita ce albarkar da Musa, mutumin Allah, ya sa wa Isra'ilawa kafin ya rasu.


Ya amsa ya ce, “Salama na tare da ku, kada ku ji tsoro, Allahnku da Allah na mahaifinku ne kaɗai ya sa muku dukiyar cikin tayakanku. Na karɓi kuɗinku.” Sai ya fito musu da Saminu.


Allah ya ba ka daga cikin raɓar sama, Daga cikin ni'imar ƙasa, Da hatsi a yalwace da ruwan inabi.


Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu,


Ubangiji zai arzuta mu, Ƙasarmu kuwa za ta ba da amfanin gona mai yawa.


har kuma in sāke komowa gidan mahaifina da salama, da Ubangiji ya zama Allahna,


Muhimmin abu na farko, sai ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, da kuma adalcinsa, har ma za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa.


sa'an nan mu tashi mu haura zuwa Betel, domin in kafa bagade ga Allah wanda ya taimake ni a kwanakin ƙuncina, wanda kuwa yake tare da ni duk inda na tafi.”


Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja, Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja, Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.


A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.


Allah Maɗaukaki ya sa maka albarka, ya sa ka hayayyafa ya riɓaɓɓanya ka, ka zama ƙungiyar jama'o'i,


Sai Yakubu ya ce, “Ya Allah na kakana Ibrahim, da mahaifina Ishaku, Ubangiji, wanda ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuwa yi maka alheri,’


Yakubu ya ce wa Yusufu, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan'ana ya sa mini albarka,


Ya kuma ce, “Allah na ubanan shi ne ya taimake ni, ya cece ni daga takobin Fir'auna,” saboda haka ya raɗa wa ɗayan, suna, Eliyezer.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ