Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma'ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.
Sai suka ce wa junansu, “A ainihin gaskiya, muna da laifi dangane da ɗan'uwanmu, da yake mun ga wahalar da yake sha, sa'ad da kuma ya roƙe mu mu taimake shi, amma ba mu saurara ba, domin haka wannan wahala ta sauko mana.”