Don haka Allah na Isra'ila ya zuga Ful, Sarkin Assuriya, wato Tiglat-filesar, ya zo ya kwashe su, ya kai su bauta, wato su Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa. Ya kai su Hala, da Habor, da Hara, har zuwa kogin Gozan, can suke har yau.
Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, sun karɓi nasu gādo wanda Musa ya ba su a hayin Urdun wajen gabas. Abin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba su ke nan,
Ga yadda aka lasafta su bisa ga matsayinsu, da Ezer, da Obadiya, da Eliyab, da Mishmanna, da Irmiya, da Attai, da Eliyel, da Yohenan, da Elzabad, da Irmiya, da Makbannai.