Sa'ad da wannan ya faru, kowa zai ce, “Shi Allahnmu ne! Mun dogara gare shi, ya kuwa cece mu. Shi ne Ubangiji. Mun dogara gare shi, yanzu kuwa muna da farin ciki domin ya cece mu!”
To, akwai wani mutum a Urushalima, mai suna Saminu, adali, mai bautar Allah, yana kuma ɗokin ganin ta'aziyyar Isra'ila. Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.
Ina addu'a matuƙa domin ceto ya zo ga Isra'ila daga Sihiyona! Sa'ad da Ubangiji ya sāke arzuta jama'arsa, Zuriyar Yakubu za su yi farin ciki, Jama'ar Isra'ila za su yi murna.
Yusufu ya zo, mutumin Arimatiya, wani ɗan majalisa mai mutunci, wanda shi ma yake sauraron bayyanar Mulkin Allah, ya yi ƙarfin hali ya shiga wurin Bilatus, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.