16 “Dan zai zama mai mulki ga mutanensa Kamar ɗaya daga cikin kabilan Isra'ila.
16 “Dan zai tanada adalci wa mutanensa kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.
A kan Dan, ya ce, “Dan ɗan zaki ne, Mai tsalle daga Bashan.”
Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni, ya ji muryata, ya kuwa ba ni ɗa.” Saboda haka ta raɗa masa suna Dan.
Samson ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin a zamanin da Filistiyawa suke mulkinsu.
Akwai wani mutumin Zora daga kabilar Dan, sunansa Manowa, matarsa bakarariya ce, ba ta haihuwa.
A ƙarshe sai ƙungiyar mutanen Dan da take bayan dukan zangon, ta tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Shugaban rundunarsu Ahiyezer ne, ɗan Ammishaddai.
Saboda ya ga wurin hutawa ne mai kyau, Ƙasar kuma mai kyau ce, Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa domin ɗaukar kaya, Ya zama bawa, yana yin aiki mai wuya.
Dan zai zama maciji a gefen hanya, Zai zama kububuwa a gefen turba, Mai saran diddigen doki Don mahayin ya fāɗi da baya.