Na kabilar Issaka akwai shugabanni ɗari biyu, waɗanda suka gane da halin da ake ciki, da abin da ya kamata Isra'ila ya yi. Su ne suke shugabancin 'yan'uwansu.
Bayan mutuwar Abimelek, sai Tola, ɗan Fuwa, ɗan Dodo, daga kabilar Issaka ya tashi don ya ceci Isra'ilawa. Ya zauna a Shamir, a ƙasar tuddai ta Ifraimu.