Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 49:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba, ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba, sai ya zo ga wanda yake mai shi. Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 49:10
58 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ina ganinsa, amma ba yanzu ba, Ina hangensa, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga cikin Yakubu, Kandiri zai fito daga cikin Isra'ila, Zai ragargaje goshin Mowabawa, Zai kakkarya 'ya'yan Shitu duka.


Ga shi, an haifa mana ɗa! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al'ajabi,” “Allah Maɗaukaki,” “Uba Madawwami,” “Sarkin Salama.”


Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.


Gileyad tawa ce, har da Manassa ma, Ifraimu ne kwalkwalina, Yahuza kuma sandana ne na sarauta.


Dukan kayayyakin waɗannan jiragen ruwa ba su da amfani, tafiyarsu ba za ta yi nisa ba! Za a kwashe dukan dukiyar sojojin abokan gāba. Za ta yi yawa har sauran jama'a za su sami rabonsu. Ubangiji kansa shi zai zama sarkinmu, zai mallake mu, ya kiyaye mu.


Tabbatacce ne, cewa Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuza ne, Musa kuwa bai ce kome ba a game da kabilar nan a kan zancen firistoci.


Za su bi ta cikin tekun wahala, Zan kwantar da raƙuman teku, Kogin Nilu zai ƙafe duk da zurfinsa, Za a ƙasƙantar da Assuriya, Sandan sarautar Masar zai rabu da ita.


Halaka, halaka, zan hallakar, ba za a bar ko alama ba, sai mai shi ya zo, shi ne zan ba shi.”


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Ishaya kuma ya ce, “Tsatson Yesse zai bayyana, Wanda zai tashi yă mallaki al'ummai, A gare shi ne al'ummai za su sa zuciya.”


Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukan mutane gare ni.”


“A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki.


Sarkinsu zai zama ɗaya daga cikinsu, Mai mulkinsu kuma zai fito daga cikinsu. Zan kawo shi kusa, zai kuwa kusace ni, Gama wane ne zai yi ƙarfin hali ya kusace ni? Ni Ubangiji na faɗa.


Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.


Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu ba mu da sarki sai Kaisar.”


Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”


Ubangiji yana sanarwa ga dukan duniya, Cewa, “Ku ce wa jama'ar Urushalima, Ubangiji Mai Cetonku yana zuwa, Yana kawo mutanen da ya cece su.”


Ubangiji ya ce, “Ifraimu ta kewaye ni da ƙarairayi, Jama'ar Isra'ila kuwa ta kewaye ni da munafuncinta, Yahuza kuma ta tayar wa Allah, Wato tana gāba da Mai Tsarki, mai aminci.


Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana, Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!


A kwanaki masu zuwa, Dutse inda aka gina Haikali zai zama mafi tsayi duka. Al'ummai da yawa za su zo su yi ta bumbuntowa su zo gare shi.


Gileyad tawa ce, har da Manassa ma, Ifraimu ne kwalkwalina, Yahuza kuma sandana ne na sarauta.


Rijiyar da hakimai suka haƙa, Shugabannin jama'a suka haƙa, Da sandan sarauta, Da kuma sandunansu.” Daga cikin jejin suka tafi har zuwa Mattana.


Za a tara dukan al'ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki.


Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”


Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”


Zan kuma girgiza al'umman duniya duka don dukiyar al'umman duniya ta samu. Zan kuwa cika Haikalin nan da daraja.


Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.


Wuta ta fito daga jikinta Ta cinye rassanta da 'ya'yanta, Don haka ba wani reshe mai ƙarfi da ya ragu, wanda zai zama sandan mulki. Wannan makoki ne, ya kuwa tabbata makoki.’ ”


Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.


A kan wannan Bilatus ya nemi ya sake shi, sai dai Yahudawa suka ɗau kururuwa suna cewa, “In dai ka saki wannan, kai ba masoyin Kaisar ba ne. Ai, kowa ya mai da kansa sarki, ya tayar wa Kaisar ke nan.”


Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa a kan kowa.”


Rassanta masu ƙarfi sun zama sandunan masu mulki, Ta yi tsayi zuwa sama duk da rassan, Ana hangenta daga nesa.


ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” wato aikakke. Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani.


A ɓoye za ta ci mahaifar da take biyo bayan ta haihu, da 'ya'yan da za ta haifa, saboda ba ta da wani abinci lokacin da magabtanku za su kewaye garuruwanku da yaƙi mai tsanani.


sa'an nan zan ƙi zuriyar Yakubu da bawana Dawuda. Ba kuma zan zaɓi wani daga cikin zuriyarsa ya yi mulkin zuriyar Ibrahim, da ta Ishaku, da ta Yakubu ba. Amma zan mayar musu da arzikinsu, in nuna jinƙai a kansu.”


Yakubu zai yi mulki, Zai hallaka waɗanda suka ragu cikin birni.”


Shi ne zai gina mini ɗaki. Ni kuwa zan tabbatar da kursiyin sarautarsa har abada.


Gidanka kuwa da mulkinka za su dawwama a gabana har abada. Gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”


Mutanen Yahuza waɗanda suke riƙe da garkuwoyi da māsu don yaƙi, mutum dubu shida da ɗari takwas (6,800).


Suka yi kwana uku tare da Dawuda, suka yi ta ci suna sha, gama 'yan garin sun shirya wata liyafa dominsu.


Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara? Wa zai kai ni Edom?


A maimakonsu sai ya zaɓi kabilar Yahuza. Ya zaɓi Dutsen Sihiyona, wanda yake ƙauna ƙwarai.


“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.


Za ka zama itacen wuta, za a zubar da jininka a tsakiyar ƙasar. Ba za a ƙara tunawa da kai ba, ni Ubangiji na faɗa.’ ”


Ki tattara sojojinki, gama an kewaye mu da yaƙi. Za su bugi kumatun Sarkin Isra'ila da sanda.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ