Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 48:4 - Littafi Mai Tsarki

4 ya ce mini, ‘Ga shi, zan sa ka hayayyafa, in riɓaɓɓanya ka, zan maishe ka ƙungiyar al'ummai, zan kuwa ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka ta zama madawwamiyar mallaka.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 ya kuma ce mini, ‘Zan sa ka yi ta haihuwa ka kuma riɓaɓɓanya, za ka ƙaru a yawa. Zan mai da kai al’ummar mutane, zan kuma ba ka wannan ƙasa tă zama madawwamiyar mallaka ga zuriyarka a bayanka.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 48:4
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”


Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka hayayyafa ka riɓaɓɓanya, al'umma da tattaruwar al'ummai za su bumbunto daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka.


Sa'ad da Maɗaukaki ya ba al'ummai gādonsu, Sa'ad da ya raba 'yan adam, Ya yanka wa mutane wurin zama bisa ga yawan Isra'ilawa.


Amma 'ya'yan Isra'ila suka hayayyafa, suka ƙaru ƙwarai, suka riɓaɓɓanya, suka ƙasaita ƙwarai da gaske, har suka cika ƙasar.


Ta haka fa Isra'ila ya yi zamansa a ƙasar Masar a ƙasar Goshen, suka kuwa sami mahalli a cikinta suka hayayyafa suka riɓaɓɓanya ƙwarai.


Sai ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama a can zan maishe ka babbar al'umma.


Gama ka riga ka ce, ‘Zan yi maka alheri, in kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar yashin teku, waɗanda ba su lasaftuwa saboda yawansu.’ ”


Allah Maɗaukaki ya sa maka albarka, ya sa ka hayayyafa ya riɓaɓɓanya ka, ka zama ƙungiyar jama'o'i,


Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya duka za su sami albarka,


hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,


Duka biyu, da wanda aka haifa daga gidanka, da wanda ka saya da kuɗi, za a yi musu kaciya. Da haka alkawarina zai kasance cikin jikinku, madawwamin alkawari ke nan.


Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.


Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir'auna biranen ajiya, wato Fitom da Ramases.


Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina.


'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji, Albarka ce ta musamman.


Zan arzuta ka ainun, daga gare ka zan yi al'ummai, daga gare ka kuma sarakuna za su fito.


Za su zauna a ƙasar da kakanninsu suka zauna, wadda na ba bawana Yakubu. Su da 'ya'yansu da jikokin 'ya'yansu za su zauna a can har abada. Bawana Dawuda kuwa zai sarauce su har abada.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ