Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama'arsa, waɗanda suka riga shi.
Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.”