Suka kuma ce wa Fir'auna, “Ranka ya daɗe, mun zo baƙunci ne cikin ƙasar, gama ba wurin kiwo domin garkunan bayinka, gama yunwa ta tsananta a ƙasar Kan'ana. Yanzu muna roƙonka, ka yarda wa bayinka su zauna a ƙasar Goshen.”
Ƙasar Masar tana gabanka. Ka zaunar da mahaifinka da 'yan'uwanka a ƙasa mai kyau, bari su zauna a ƙasar Goshen. In kuma ka san da waɗansu waɗanda suka dace a cikinsu, ka sa su su lura da shanuna.”