sai ya tattara dukan abinci na shekarun nan bakwai da aka yi na ƙoshi a ƙasar Masar, ya kuwa tanada abinci cikin birane, a kowane birni ya tanada abinci daga karkarar da take kewaye da shi.
Ta haka Yusufu ya saya wa Fir'auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da saurukansu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama halaliyar Fir'auna.
Sai gonakin firistoci ne kaɗai bai saya ba, gama firistocin suna da rabo wanda Fir'auna ya yanka musu, da rabon da Fir'auna yake ba su suke zaman gari, sabili da haka ba su sayar da gonakinsu ba.