Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 47:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Saboda haka suka kai wa Yusufu dabbobinsu, sai Yusufu ya ba su abinci madadin dawakai da garkunan awaki da na tumaki, da garkunan shanu da na jakai, ya tallafe su da abinci a madadin dabbobinsu duka a wannan shekara.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Saboda haka suka kawo dabbobinsu wa Yusuf, ya kuma ba su abinci a madadin dawakai, tumaki da awaki, shanu da jakunansu. Ya kuwa ba su abinci a madadin dabbobinsu, a wannan shekara.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 47:17
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”


Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba.


Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Mutum ya iya rabuwa da dukan abin da yake da shi don yă ceci ransa.


Sulemanu kuwa ya sayo dawakai daga Masar da Kuye. 'Yan kasuwar sarki sukan sayo dawakai daga Kuye a kan tamaninsu.


to, hannuna zai auka wa dabbobinka cikin sauruka, da dawakai, da jakai, da raƙuma, da shanu, da tumaki, da awaki, da annoba mai tsanani.


Yusufu ya amsa, ya ce, “Ku ba da shanunku, ni kuwa zan ba ku abinci a madadin shanunku in kuɗinku sun ƙare.”


Sa'ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biyu, suka ce masa, “Ranka ya daɗe. Ba za mu ɓoye wa shugabanmu ba cewa kuɗinmu duka mun kashe, garkunan dabbobin kuma sun zama naka. Banda jikunanmu da gonakunmu, ba kuwa abin da ya rage mana.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ