Sa'an nan dukan jama'a suka haye Urdun, sarki kuma ya haye. Ya yi bankwana da Barzillai, ya sumbace shi, ya kuma sa masa albarka. Sai Barzillai ya koma gidansa.
sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda don ya gaishe shi, ya kuma yaba masa saboda ya ci Hadadezer da yaƙi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi kullum. Adoniram kuwa ya kawo wa Dawuda kyautar kayan azurfa, da na zinariya, da na tagulla.
Sai Yusufu ya zaunar da mahaifinsa da 'yan'uwansa, ya kuwa ba su mahalli a ƙasar Masar, cikin ƙasa mafi kyau a ƙasar Remesse, kamar yadda Fir'auna ya umarta.