Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 46:7 - Littafi Mai Tsarki

7 'ya'yansa maza da jikokinsa maza tare da shi, 'ya'yansa mata, da jikokinsa mata, ya kawo zuriyarsa dukka zuwa ƙasar Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ya ɗauki ’ya’yansa maza da jikokinsa da ’ya’yansa mata da jikokinsa mata, dukan zuriyarsa zuwa Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 46:7
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka kuma kora shanunsu, suka ɗauki kayayyakinsu waɗanda suka samu a ƙasar Kan'ana, suka iso Masar, Yakubu da zuriyarsa duka,


Waɗannan su ne sunayen 'ya'ya maza na Isra'ila, wato Yakubu, waɗanda suka iso Masar. Ra'ubainu, ɗan farin Yakubu.


Ishaku kuma na ba shi Yakubu da Isuwa. Na kuma ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir, ya mallake ta, amma Yakubu da 'ya'yansa suka gangara zuwa Masar.


'Ya'yan Yakubu, maza, kuwa sa'ad da suka komo daga saura, da suka ji yadda aka yi, sai suka hasala, abin ya ba su haushi ƙwarai, don Shekem ya yi aikin wauta ga Isra'ila da ya kwana da 'yar Yakubu. Gama irin wannan abu, bai kamata a yi shi ba.


yadda kakanninmu suka gangara zuwa Masar, suka zauna a can da daɗewa, da yadda Masarawa suka wahalshe mu, mu da kakanninmu.


“Kada ku ji ƙyamar Ba'edome gama shi danginku ne. Kada kuma ku ji ƙyamar Bamasare don kun yi baƙunci a ƙasarsa.


Sa'an nan kuma sai ku hurta waɗannan kalmomi a gaban Ubangiji Allahnku, ku ce, ‘Ubana Ba'aramiye ne, mayawaci a dā. Ya gangara zuwa Masar yana da jama'a kima, ya yi baƙunci a wurin. Amma a can ya zama al'umma mai girma, mai iko, mai yawa.


Sa'an nan Yakubu ya tafi Masar, Ya zauna a ƙasar.


Kuka taɓa zaman baƙuntaka a Masar, Daga baya Assuriyawa suka zalunce ku ba gaira ba dalili.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ