Na kabilar Issaka akwai shugabanni ɗari biyu, waɗanda suka gane da halin da ake ciki, da abin da ya kamata Isra'ila ya yi. Su ne suke shugabancin 'yan'uwansu.
'Ya'yan Yahuza, maza, su ne Er, da Onan, da Shela, da Feresa, da Zera, (amma Er da Onan suka rasu a ƙasar Kan'ana). 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.